fbpx

Shin Farfesa Ibrahim Gambari zai iya kawo sauyi a gwamnatin Buhari ?


Ibrahim GambariHakkin mallakar hoto
Getty Images

Naɗin da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi wa Farfesa Ibrahim Gambari a matsayin sabon shugaban ma’aikatan fadar shugaban Najeriya ya bai wa mutane da dama mamaki.

Ko da yake akasarin masu sharhin siyasa ba sa shakkar ƙwarewar Farfesa Gambari wajen aiwatar da ayyukansa, kasancewarsa tsohon fitaccen jami’in difilomasiyya kuma tsohon shugaban jami’a.

Sai dai ba ya cikin mutanen da ake kallo a matsayin na kurkusa da Shugaba Buhari da aka yi zaton za a ba wannan mukami, duk da cewa ya taɓa zama ministan wajen Najeriya lokacin mulkin soji na Janar Muhammadu Buhari tsakanin 1984 zuwa 1985.

Kazalika wasu ‘yan ƙasar suna kallon Farfesan, ɗan asalin jihar Kwara mai shekara 75, a matsayin mutumin da shekarunsa suka ja don haka naɗinsa ya zo da ba-zata ganin cewa an yi tsammanin Shugaba Buhari zai naɗa matashi ko kuma wanda shekarunsa ba su haura sosai ba.

Hasali ma, ‘yan Najeriya da dama sun yi tsammanin shugaban na Najeriya zai naɗa mutane irin su Ministan Ilimi, Adamu Adamu; Shugaban Hukumar Kwastam, Kanal Hameed Ali da kuma fitaccen ɗan siyasa Ambasada Babagana Kingibe ne.

Dukkansu ana ganin suna da matuƙar kusanci da shi, kuma an yi ta raɗe-raɗin cewa kamar sun nuna sha’awar samun mukamin.

Wasu rahotanni na cewa mutane kimanin 20 ne suka nuna sha’awarsu ta darewa wannnan kujera.Masu lura da al’amura da dama na ganin akwai ƙalubale da dama a gaban Farfesa Gambari wajen tafiyar da ayyukan fadar shugaban Najeriya musamman ganin yadda aka zargi magabacinsa da ma wasu a cikin fadar da hannu wajen juya akalar Shugaba Muhammadu Buhari.

Farfesa Ibrahim Gambari fitaccen malamin jami’a ne kuma ma’aikacin diflomasiyya da ya rike mukamai manya-manya a duniya da Afirka da kuma Najeriya. Dr Abubakar Kari, wani mai sharhi kan harkokin siyasa kuma Malami a Jami’ar Abuja ya shaida wa BBC cewa akwai jan aiki a gaban Farfesa Gambari musamman yadda Shugaba Buhari ya taɓa umartar jami’an gwamnatinsa da ministoci su miƙa duk wani batu da ya shafi ganawa da shi ga shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasar.

“Wannan muƙami yana da ƙima sosai a gwamnatin Shugaba Buhari tun da kusan za a ce shi ne zai haɗa hancin dukkan ayyukan da suke faruwa a fadar;

Wanda ya gada an ba shi karin aiki inda aka ce duk wanda zai je wurin shugaban kasa hatta ministoci sai sun gan shi tukunna” yana mai cewa “sa’a ashirin da huɗu sun yi masa kaɗan” a kullum wajen gudanar da ayyukan fadar ta shugaban ƙasa.

Rayuwar Farfesa Ibrahim Gambari a takaice

 • An haifi Ibrahim Gambari a shekarar 1944, a Ilorin, jihar Kwara da ke arewa ta tsakiyar Najeriya.
 • Gambari ya yi sakandarensa a King’s College da ke Lagos. Ya yi digirinsa na farko a London School of Economics inda ya kammala a 1968 kuma ya samu kwarewa a fannin harkokin kasashen waje.
 • Ya yi digirinsa na biyu da na uku a 1970 da 1974 a jami’ar Columbia University, New York da ke Amurka a fannin kimiyyar siyasa da harkokin kasashen waje.
 • Daga nan sai Farfesa Gambari ya koma jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria a jihar Kaduna inda ya koyar daga 1977 zuwa 1980.
 • Farfesa Ibrahim Gambari ya kasance mutum na farko da ya zama Magatakardan Sakataren Majalisar Dinkin Duniya kuma mai ba da shawara na musamman ga Sakatare Janar na Tarayyar Afirka,
 • A shekarar 1984 zuwa 1985 Ibrahim Gambari ya zamo ministan harkokin wajen Najeriya.
 • Ibrahim Gambari ya sake zama ambasada kuma wakilin Najeriya na dindindin a Majalisar Dinkin Duniya a 1990 zuwa 1999.
 • A 1999 din dai Gambari ya kasance Shugaban Kwamitin gudanarwa na UNICEF.
 • Gambari ya jagoranci kwamitin wanzar da zaman lafiya na hadin gwiwa tsakanin Majalisar Dinkin Duniya da Tarayyar Afirka a Darfur daga 2010 zuwa 2012.
 • Ya taba lashe karramawar Shugaban Afirka ta Kudu, Jacob Zuma ga wadanda ba ‘yan kasa ba a 2012.
 • Farfesa Ibrahim Gambari ya zamo shugaban jami’ar jihar Kwara na farko a 2013.
 • Ibrahim Gambari ne mutumin da ya kafa cibiyar bincike ta Savannah Centre for Abuja.

A cewar Dr Kari dole masanin na difilomasiyya ya yi taka-tsantsan wajen hulɗa da jama’a da kuma kare muradun Shugaba Buhari saboda yadda aka samu rarrabuwar kawuna tsakanin ɓangarori da dama da ke fadar shugaban ƙasar.

Inda ko a baya wasu ke kallon marigayi Abba Kyari da wasu makusanta Shugaba Buhari da juya al’amuran ƙasar da kuma hana ruwa gudu.Hasali ma, wani mai sharhi kan al’amura, Farfesa Farooq Kperogi, yana ganin wani bangare ne na masu ruguguwar neman iko a fadar shugaban kasar ya yi sanadin nada Farfesa Gambari kan mukamin don haka babu abin da zai sauya, ko da yake wasu na ganin Farfesan ba zai bari kowa ya juya shi ba.Jim kadan da bayyana nada shi a mukamin, Furofesa Ibrahim Gambari wanda tsohon babban jami’i ne a Majalisar Dinkin Duniya, ya shaida wa manema labarai cewa zai yi wa shugaba Buhari cikakkiyar biyayya.

Ya ce Shugaba Buhari “yana bukuatar biyayyata, da kwarewata da kuma goyon bayana.” Furofesa Gambari ya yi wa shugaban kasar godiya saboda damar da ya ba shi ta yi masa aiki da kuma yi wa kasa hidima.

To amma sabon shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasar ya ce bisa tsarin mukamin, ba ga ‘yan Najeriya zai rika yin bayani kai tsaye game da aikinsa ba, a’a, ga Shugaba Buhari ne.Wani batu kuma da Farfesa Gambari zai fuskanta shi ne na zabar mutumin da zai maye gurbin shugaba Buhari a 2023 lokacin da wa’adin mulkin shugaban kasar zai kare.Masu lura da lamura na ganin duk wanda yake rike da mukamin shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasar zai iya yin tasiri wajen tsayar da mutumin da zai maye gurbin Shugaba Buhari.

“Na uku kuma shi ne ita kanta gwamnatin tana fama da kalubale daban-daban…gwamnati ce wadda ‘yan Najeriya suka sanya mata ido ganin cewa za ta magance manya da kananan matsaloli amma kuma hakan bai kasance ba”, in ji Dr Kari.Sai dai masana harkokin yau da kullum na ganin Farfesa Gambari zai yi amfani da kwarewarsa wajen fitar da ‘yan Najeriya daga mawuyacin halin da suke ciki, musamman kasancewarsa mutum da ke da gogewa kan sha’anin mulki da difilomasiyya da kuma sanin manyan mutane masu faɗa-a-ji a Najeriya da kuma sassa daban-daban na duniya.

Hakkin mallakar hoto
Twitter/@NGRPresidentSource link

Leave a Reply

%d bloggers like this: