fbpx

Coronavirus: Shugabannin ƙasashen da ba sa sanya takunkumi


Trump da Buhari da Boris JohnsonHakkin mallakar hoto
Getty Images

Abin rufe baki da hanci ko takunkumi, yanzu ya kusan zama wani abin da mutane suka saba da shi musamman a ƙasashen da aka tilasta amfani da shi, ɗaya daga cikin matakan kariya daga kamuwa da cutar korona, annoba a duniya.

Sai dai duk da tilasta amfani da takunkumin da wasu gwamnatocin ƙasashe suka yi, amma akwai shugabannin da ba a gani sanye da takunkumin a duk lokacin da suka fito bainar jama’a.

Kuma shugaban Amurka Donald Trump da takwaransa na Najeriya Muhammadu Buhari da Firaministan Birtaniya Boris Johnson suna cikin shugabannin da ba a taba ganinsu sanye da takunkumi ba.

Ko da yake Hukumar Lafiya ta duniya WHO ta ce takunkumin yana hana yaɗuwar cutar korona amma kuma ba wata babbar kariya ba ce ga hana kamuwa da cutar.

Watakila shi ne dalilin da ya sa shugabannin ba su damu da saka takunkumin ba, duk da sun umurci al’ummar kasarsu su dinga sakawa.

A jawabinsa na uku ga ‘yan Najeriya kan cutar korona, Shugaba Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da tabbatar da ganin ana amfani da takunkumi ko abin rufe fuska a bainar jama’a da kuma ci gaba da ba da tazara da tsaftar jiki.

Shugaban na Najeriya ya kuma buƙaci gwamnatocin jihohi da kamfanoni da masu zuciyar taimakawa jama’a su tallafa wajen samar da takunkuman ga al’ummar ƙasa. Amma ba a taba nuna shugaba Buhari sanye da takunkumin ba domin koyi da shi.

Akwai hoto da na bidiyo da aka nuna shugaban yana wanke hannayensa – ɗaya daga cikin matakan kariya daga kamuwa da cutar korona da ake son a dinga yi a ko da yaushe.

Amma batun saka takunkumin ya janyo mahawara a shafin Facebook na BBC Hausa inda wasu ƴan ƙasar ke yaba wa da umurnin saka takunkumin, wasu kuma ke ganin ya kamata ace an yi koyi da shugaban.

Duk da Boris Johnson ya warke daga cutar korona amma ba a taɓa nuna Firaministan na Birtaniya ba sanye da takunkumi.

Cutar korona ta kashe mutum sama da dubu talatin a Birtaniya, yayin da sama da mutum dubu 230 suka kamu da cutar.

Takunkumi bai zama dole ba – Trump

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Shugaba Trump na Amurka yana ganin sanya abin rufe baki da hanci bai zama dole ba.

A watan Afrilu da hukumomin lafiya a Amurka suka bukaci sanya takunkumi, Trump ya ce ba da shi ba.

Trump ya ce ba zai yi kyau ya sa takunkumi a ofishinsa ba yayin da yake ganawa da shugabannin duniya.

Ya kuma ci gaba da cewa shawara ce daga hukumar daƙile cutuka masu yaduwa ta kasar CDC cewa ba lallai ne shi sai ya sa takunkumin ba.

Yanzu haka dai ma’aikatan Fadar White House an tilasta masu amfani da takunkumi bayan wasu jami’ai biyu mataimaka na musamman ga mataimakin shugaban Amurka Mike Pence da kuma shugaba Trump sun kamu da korona.

Hakkin mallakar hoto
Présidence de la République du Niger

Image caption

Shugaba Mahamadou Issoufou na Nijar sanye da takunkumi

Trump ya ce shi ya bukaci kafa dokar a Fadar White House.

Cutar korona ta fi kashe mutane a Amurka fiye da sauran ƙasashe a duniya inda sama da mutum dubu tamanin suka mutu yayin da sama da mutum miliyan daya da dubu dari hudu suka kamu da cutar zuwa yanzu.

Hukumar Lafiya ta duniya WHO ta bukaci yin amfani da abin rufe baki da hanci idan mutum na kusa da mai cutar korona. Ko kuma idan mutum na tari da atishawa. Amma wanda ba ya ɗauke da cutar ba lalle ne sai ya saka ba.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Shugaban Faransa Emmanuel MacronSource link

Leave a Reply

%d bloggers like this: